Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya ci wa kasarsa kwallo ta 99

Cristiano Ronaldo ya ci wa kasarsa ta Portugal kwallo ta 99, yayin wasan da suka lallasa Luxemborg da 2-0, nasarar da ta basu tikitin cancantar halartar gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai da za a yi cikin watan Yunin shekara mai kamawa.

Kaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo.
Kaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo. MIGUEL A. LOPES/LUSA
Talla

Bruno Fernandez ya soma ciwa Portugal din kwallo ta farko, kafin Ronaldo ya kara, abinda ya sa Portugal komawa matsayi na 2 a rukunin B da take, wanda kasar Ukraine ke jagoranta, bayan da a jiya ta tashi 2-2 tsakaninta da Serbia.

A bangaren Cristiano Ronaldo kuwa, ya kama hanyar kafa tarihin zama dan wasan da ya fi kowanne ci wa kasarsa kwallaye inda a yanzu yake da kwallaye 99, bayan da a ranar Alhamis din data gabata, ya ci uku daga cikin kwallaye 6-0 da Portugal ta lallasa Lithuania da su yayin wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Turai.

Har yanzu dai dan wasan gaba na Iran Ali Daei ne ke rike da kambin adadin kwallaye mafi yawa da ya ci wa kasarsa, bayanda a tsakanin shekarun 1993 zuwa 2006 ya ci kwallayen 109.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.