Isa ga babban shafi
Wasanni

Halin da ake ciki a Gasar Cin Kofin Duniya a Brazil

Wallafawa ranar:

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya sake waiwayar wainar da ake tuyawa a Gasar Cin Kofin Duniya ta Matasa 'yan kasa da shekaru 17 da ke gudana a Brazil, inda  kasashe irinsu Najeriya da Brazil mai masaukin baki da Faransa da Angola da Senegal suka samu gurbi a zagaye na biyu na gasar. Shirin ya kuma duba kalubalen da ke gaban gasar firimiyar Najeriya a daidai lokacin da aka fara gudanar da ita a karshen mako. Kazalika za ku ji fashin bakin masana dangane da koma-bayan da Barcelona da Real Madrid ke fuskanta a kakar bana.

Najeriya ce ta fi kowacce kasa lashe kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17,inda ta dauka har sau biyar.
Najeriya ce ta fi kowacce kasa lashe kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17,inda ta dauka har sau biyar. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.