Gasar Cin Kofin Duniya ta Matasa a Brazil
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan Gasar Cin Kofin Kasashen Duniya ta Matasa 'Yan kasa da Shekaru 17 da ke gudana a Brazil, inda tuni Najeriya da ke neman lashe kofin gasar karo na shida, ta yi ruwan kwallaye a wasanta na farko da Hungary.