Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Neymar ya bugawa Brazil wasa na 100 yayin wasansu da Senegal

Dan wasan gaba na Brazil da ke taka leda a PSG ta Faransa ya yi nasarar dokawa kasarsa wasanni 100 yayin wasan da Brazil ta yi canjaras da Senegal a jiya Alhamis a wani wasan sada zumunta da ya gudana tsakaninsu a Singapore.

Neymar na Brazil da Sadio Mané na Sénégal
Neymar na Brazil da Sadio Mané na Sénégal © REUTERS/Feline Lim
Talla

Neymar mai shekaru 27 ya zamo dan wasa mafi karancin shekaru a tarihin Brazil da zai dora akan wasanni 100 a bangaren kasarsa.

Duk da cewa dai yayin wasan na jiya tsakanin Brazil da Senegal Neymar bai yi nasarar zura kwallo ko guda ba, amma wasan zai zamo na tarihi a gareshi.

A wasan dai Roberto Firmino ne ya yi nasarar zura kwallon daya tal a minti na 8 da fara wasa amma kuma Famara Diedhiou ya farke gab da tafiya hutun rabin lokaci sakamakon bugun fenaritin da aka bashi bayan da dan wasan Brazil ya shatale Sadio Mane lokacin da yak e gab da zura kwallo a ragar Brazil, inda aka tashi wasa 1-1.

A tsawon wasannin da Neymar ya bugawa kasarsa ya yi nasarar zura kwallaye 61 inda ya dara Ronaldo de Lima da kwallo guda, ko da dai ya na bukatar kwallo 16 don kamo Pele wanda shi wasanni 92 cal ya iya dokawa kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.