Isa ga babban shafi
Wasanni

Wakilan Neymar da Barcelona sun gana kan takaddamar sauyin sheka

Lauyoyin tauraron kwallon kafar PSG da kuma Brazil, Neymar, sun gana da wakilan tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, domin warware takaddamar dake tsakaninsu kan sauyin shekar da dan wasan yayi daga Spain zuwa Faransa a 2017.

Tauraron dan wasan kungiyar PSG, Neymar Jr.
Tauraron dan wasan kungiyar PSG, Neymar Jr. ®REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Matakin da Neymar ya dauka na rabuwa ra Barcelona cikin ba zata duk dacewa bai dade da sanya mata hannu kan sabuwar yarjejeniya ba daza ta kare a 2021, ya fusata kungiyar, inda Barcelonan ta garzaya kotu don neman a hukunta Neymar kan aikata laifin cin amana da karya dokokin yarjejeniyar da suka kulla.

A waccan lokacin dai Barcelona ta ki biyan Neymar euro miliyan 26 dake cikin tagomashin sabuwar yarjejeniyar daya kulla da ita.

To sai dai a baya bayan bangarorin biyu, suka soma tattaunawar sulhu da nufin kaucewa ci gaba da shari’ar da ka iya lakumewa kowanne makudan kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.