Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA za ta sauya dokokin bada aron 'yan wasa da kudaden wakilai

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta amince da sabuwar dokar takaita yawan ‘yan wasan da kungiyoyi za su rika bayarwa a matsayin aro, da kuma rage yawan kudaden da ake baiwa wakilan ‘yan wasa da kungiyoyi a matsayin ladan aikinsu.

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino. Reuters
Talla

Yayin da take bayyana matakin a ranar laraba, FIFA ta ce dokokin za su soma aiki ne daga kakar wasa ta badi.

Yadda abin yake kuwa shi ne, a kakar wasa ta badi, adadin ‘yan wasan da kowace kungiya take da damar baiwa wata a matsayin aro zai kuma takwas a maimakon adadin da ta ga dama.zuwa kakar wasa ta 2022/2023 adadin zai koma 6.

FIFA tace daukar matakin ya zama dole, domin kawo karshen yadda manyan kungiyoyi ke boye ‘yan wasa masu yawa, ta hanyar mika su aro, inda ta bada misalin kungiyar Monaco da a yanzu haka take daadadin ‘yan wasa 18 dake wasu kungiyoyi a matsayin aro.

Dangane da batun kudaden da za a rika biyan wakilan ‘yan wasa a matsayin lada kuwa, FIFA tace daga kakar wasa ta badi, kungiyoyi ba za su rika biyan wakilansu a fagen ciniki, sama da kashi 10 cikin 100 na jimillar kudaden da suka karba na saida ‘yan wasansu ba.

A bangaren wakilan ‘yan wasa kuma za a rika biyansu kashi 3 cikin 100 ne kawai daga cikin jimillar kudaden da za a mikawa wanda suke wakilta, sai kuma makamancin kashi 3 na farko da kungiya mai sayen dan wasa zata biya wakili.

A 2016, an biya wakilin Paul Pogba ladan euro miliyan 27, saboda taka rawa wajen sauyen shekar dan wasan daga Juventus zuwa Manchester United kan sama euro miliyan 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.