Isa ga babban shafi

Ba ma bukatar kwaikwayon salon Manchester City a wasanmu- Klopp

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce Club din baya bukatar gasa ko kuma kwaikwayon salon Manchester City dai dai lokacin da kungiyoyin biyu ke ci gaba da tafiya kafada da kafada kamar a kakar wasa ta bara a kokarinsu na lashe kofin Firimiya.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. REUTERS/Charles Platiau
Talla

A cewar Klopp salon da City ke amfani da shi ba kowanne Club ne zai iya ba, musamman bayan nasararsu ta lallasa Watford da kwallaye 8 da banza cikin karshen makon nan, yayinda Liverpool a bangarenta ta lallasa Chelsea da kwallaye 2 da 1.

Jurgen Klopp wanda ya yabawa kokarin ‘yan wasansa ya ce nasarar ta su a jiya, babban sakamako ne, don ya dauke su lokaci mai tsayi ba su iya samun nasara kan Chelsea a gida ba.

Manajan na Liverpool ya ce tawagar za ta ci gaba da taka leda a salonta, tare da lashe makin kowanne wasa don ganin sun kai labarin dage kofin na Firimiya a wannan karon.

Ko a bara ma dai Liverpool ce ta rika jagorancin teburin na Firimiya har zuwa watan Fabarairu kafin jancaras din da ta yi sau biyu su ja mata koma bayan da ya hana mata damar dage kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.