Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ba abu ne mai sauki lashe kofin zakarun Turai a jere ba- masana

Masu sharhin wasanni na ganin abu ne mai wuya kungiyar da ke rike da kofin na zakarun Turai ta iya sake nasarar dage shi a wannan kaka, la’akari da cewa daidaikun kungiyoyi ne a tarihi suka taba iya nasarar dage kofin sau 2 a jere.

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool bayan lashe kofin zakarun Turai.
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool bayan lashe kofin zakarun Turai. REUTERS/Carl Recine
Talla

Tun bayan fara gasar a 1956 kafin sauya mata suna a 1992 kungiyoyin kwallon kafa 11 ne kadai suka iya nasarar zuwa wasannin karshe a jere, haka zalika kafin Zinadine Zidane ya yi nasarar kai Real Madrid ga nasarar dage kofin sau 3 a jere tsakanin shekarun 2016 da 2017 da kuma 2018, AC Milan ce kadai ta taba samun makamanciyar damar a shekarar 1990, bugu da kari tun daga shekarar 1992 kungiya daya ce da ke rike da kofin ta taba kafa tarihin tsallake wasannin rukuni ita ce Real Madrid

Rahotanni sun bayyana cewa ko Barcelona da ke matsayin kungiya mafi karfi tsawon shekaru, a shekara 3 ne ta iya dage kofin na zakarun Turai sau 2 karkashin jagorancin Pep Guardiola.

Sai dai akwai masu sharhin da ke ganin matukar Liverpool ta rike wuta za ta iya kai labarin kafa tarihin sake dage kofin a jere, musamman la’akari da yadda ta faro wasanninta na Firimiya a Ingila inda ta ke da maki 15 a wasanni 5 da ta doka ba tare da an yi nasara a kanta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.