Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ronaldo ya samu miliyoyin daloli a kwantiragi da wani kamfani

Wasu bayanai da aka yi katarin samunsu na nuni da cewa Cristiano Ronaldo, wanda sau biyar yana lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon D’or ta duniya zai samu kudi da ya kai Yuro miliyan 163 daga kwantiragin kamfanin Nike da ya samu, kamar yadda mujallar Der Spiegel ta ruwaito a Juma’a.

Cristiano Ronaldo lokacin da ya zura wa Atletico Madrid kwallaye uku.
Cristiano Ronaldo lokacin da ya zura wa Atletico Madrid kwallaye uku. REUTERS/Alberto Lingria
Talla

A kwantiragin baya – bayan nan da ya samu, wadda zai kai har shekarar 2026, Ronaldo zai kwashi garabasa na Yuro miliyan 4 idan ya lashe wata kyauta, kamar yadda yarjejeniyar ta nuna.

Ronaldo wanda ya koma Juventus a 2018 bayan barin Real Madrid da Manchester United, inda ya ci kyautuka da dama yana da kwantiragi da wani kamfanin yin tufafi na Amurka tun shekarar 2004, inda ya ke samun kusan Yuro miliyan 4 duk shekara.

Kamfanin Nike ya mayar da martani kan wannan rahoton da ya fito, yana mai cewa ba ya yin tsokaci kan kwantiragin dan wasa.

Dan wasan da ya fi samun kudin shiga a Jamus, Mesut Ozil shi ma ya samu shiga rahoton, inda aka ce yana samun miliyan 1 da dubu dari 2 na Yuro daga kamfanin Adidas, kudin da ya ragu da dubu dari 8 bayan ya yi ritaya daga buga wa tawagar kwallon kafar Jamus wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.