Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Har yanzu Salah ne kan gaba cikin hazikan 'yan wasan Afrika a Turai

Wani jadawalin 'yan wasan Afrika mafiya hazaka a nahiyar Turai cikin wannan kaka ya nuna cewa har yanzu Muhammad Salah na Masar na matsayin jagaba a jerin ‘yan wasan Afrikan mafiya kwazo a nahiyar Turai bayan nasararsa ta zura kwallaye har biyu a ragar Arsenal yayin wasansu na ranar asabar da aka tashi wasa Liverpool na da 3 Arsenal na da 1 a gasar Firimiya.

Muhammad Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool
Muhammad Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Baya ga Salah Jordan Ayew na Crystal Palace dan kasar Ghana shi ke matsayin na 2 bayan nasararsa ta zura kwallo 1 a ragar Manchester United da ya basu damar lallasa United din da kwallaye 2 da 1 haka zalika ya shafe tarihin 1989 rabon da Crystal Palace ta yi nasara kan Manchester United.

Dan wasa na 3 a jadawalin shi ne Moussa Djenepo dan kasar Mali da ke taka leda a Southampton wanda shima ya yi nasarar zura kwallon farko da ya baiwa Club dinsa damar nasara kan Brighton da kwallaye 2 da banza.

Akwai kuma Karl Toko Ekambi dan Kamaru da ke taka leda a Villarreal ta Spain mai doka gasar Laliga shima dai da kwallon da ya taimakawa Gerard Moreno zurawa a ragar Levante ko da dai sun yi rashin nasara hannun Lavente a wasan.

Haka zalika akwai Christian Kouame na Cote ‘D Voire da ke taka leda a Genoa mai doka gasar Serie A wanda shi ma ya taimakawa Club din samun maki 3 a wasan da suka yi canjaras da Roma da kwallaye 3-3.

Sauran sun hada da Kevin-Prince Boateng dan kasar Ghana da ke taka leda a Fiorentina wanda ya yi nasarar zura kwallo a wasanshi na farko a bangaren Fiorentina ko da dais un yi rashin nasara hannun Napoli da kwallo 3 da 4.

Sai kuma Ihlas Bebou dan kasar Togo mai taka leda a Hoffenheim wanda shima y azura kwallo a wasansa na farko a bangaren Hoffeinham inda suka yi nasara kan Werder Bremen da kwallaye 3 da 2.

Haka zalika akwai Babacar Gueye dan Senegal da ke taka leda a Paderborn wanda ya zura kwallo daya tal a wasan da suka yi rashin nasara hannun Freigburg da kwallaye 3 da 1.

Sai kuma Eric Maxim Choupo-Moting dan Kamaru na PSG wanda y azura kwallaye 2 a wasan da PSG ta lallasa Tolouse da kwallaye 4 da banza.

Jadawalin ya karkare da Islam Slimani dan Algeria da ke taka leda a Monaco wanda y azura kwallon da ta basu damar yin canjaras da Nimes da kwallaye 2 da 2 duk dai a cikin wannan makon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.