Isa ga babban shafi
Wasanni

Cantona zai karbi kyautar shugaban UEFA ta bana

Tsohon dan wasan gaba na Manchester United, Eric Cantona zai karbi kyautar shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Turai saboda gudunmawar da ya bayar ta inganta rayuwar wasu mutane.

Eric Cantona
Eric Cantona REUTERS
Talla

A ranar Alhamis mai zuwa ne,tsohon dan wasan mai shekaru 53 wanda ya buga wa Faransa wasanni 45, zai karbi wannan kyauta a birnin Monaco.

Shugaban hukumar UEFA, Aleksander Ceferin ya gamsu da irin aikin da Cantona ke yi tun bayan ritayarsa daga fagen tamaula.

A shekarar 1997 ne, Cantona ya yi ritaya bayan ya cika shekaru 30 da haihuwa, yayinda ya karkata hankalinsa kan harkar kwallon yashi da kuma fina-finai, sannan kuma yana bayar da gudunmawa ta fannin agaza wa mabukata.

Tsoffin ‘yan wasa irinsu David Beckham da Johan Cruyff da Bobby Charlton da Franz Beckenbauer da Bobby Robson da kuma Paolo Maldini sun taba lashe irin wannan kyauta ta shugaban hukumar UEFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.