Isa ga babban shafi
Wasanni

Pogba ya haramta wa United samun nasara a kan Wolves

Paul Pogba na Manchester United ya barar da bugun fanariti a wasan da Wolves ta rike su 1-1 a gasar firimiya ta Ingila.

Lokacin da Paul Pogba ya barar da bugun fanariti a wasasu da Wolverhampton Wanderers
Lokacin da Paul Pogba ya barar da bugun fanariti a wasasu da Wolverhampton Wanderers Reuters
Talla

Sai dai kocin Manchester United, OIe Gunnar Solskjaer ya ki sukar Pogba kan barar da bugun fanaritin, abinda ya haramta wa kungiyar samun nasararta ta biyu a jere a gasar kakar firimiyar bana.

Mai tsaren ragar Wolves, Rui Patricio ya yi bajintar tunkude zazzafar kwallon da Pogba ya bugo ta da karfi.

Da fari dai an zaci Marcus Rashford ne zai buga fanaritin, amma hoton bidiyo ya nuna tamkar Pogba na yi masa rada don ba shi damar bugawa.

A karo na hudu kenan da dan wasan na Manchester United ke barar da bugun fanariti tun daga kakar bara, inda a kakar da ta gabata ya zubar da fanariti har guda uku.

Solskjaer ya ki caccakar Pogba, hasalima cewa ya yi, dan wasan ya zura kwallaye da dama a bugun fanariti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.