Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar zai amince da rage albashinsa a Barcelona

Rahotanni sun ce, dan wasan Brazil, Neymar dake takawa kungiyar PSG leda, zai amince ya rage kudaden albashin da ya bukaci Barcelona ta rika biyan shi kafin komawa kungiyar domin ci gaba da taka mata leda.

Dan wasan kungiyar PSG, Neymar.
Dan wasan kungiyar PSG, Neymar. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Rahotannin sun ce, dan wasan na farin cikin zabtare euro miliyan 15 daga cikin euro miliyan 38, inda a yanzu zai karbi euro miliyan 23 muddin cinikin ya fada.

Ana ganin dai wannan wani ci gaba ne a bangaren Barcelona wadda ke matukar muradin sake dauko dan wasan, inda har ta yi tayin biyan zunzurutun pam miliyan 100 tare da Karin dan wasanta Philippe Coutinho a matsayin farashin sayen Neymar daga PSG ta Faransa.

Lionel Messi da Luis Suarez da Gerard Pique har ma da shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu dukkaninsu na matukar kaunar dawowar Neyma kungiyar.

Ita ma dai Real Madrid ta nuna yunwurta ta sayo dan wasan, inda har ta ce , za ta bayar da Gareth Bale da james Rodriuguez baya ga kudade masu yawa domin dai a mika manta Neymar din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.