Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid na tattaunawa da PSG don sayen Neymar

A yayinda ake gab da rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a Turai, jaridar Sky Sports ta rawaito cewa, Real Madrid ta bude sabuwar tattaunawa da PSG game da sayen dan wasan Brazil Neymar.

Neymar na Brazil da ke taka leda a PSG ta Faransa
Neymar na Brazil da ke taka leda a PSG ta Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Dan wasan ya hakikance cewa, yana da burin raba gari da PSG a cikin wannan kakar kamar yadda Sky Sports ta rawaito, amma ta ce, har yanzu PSG din ba ta samu kyakkyawani tayi daga wata kungiya a hukumance ba.

bayanai na cewa, PSG na bukatar kungiyar da za ta mayar mata da makudaden kudaden da ta kashe wajen dauko Neymar daga Braceolana a shekarar 2017, kudaden da yawansu ya kai Pam miliyan 200.

A bagare guda wata jaridar Spain da ake kira Sport ta rawaito cewa, Real Madrid a shirye take ta mika wa PSG Euro miliyan 110, sannan ta kara mata Luka Modric duk dai da sunan sayen Neymar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.