A cikin watan Yulin da ya gabata, Manchester United ta yi watsi da tayin Inter Milan na Pam miliyan 54 a matsayin farashin Lukaku.
A jiya Laraba ne, dillalin dan wasan, Federico Pastorello ya yi balaguro zuwa birnin London, a yunkurinsa na warware matsalar da ke tattare da makomar Lukaku.
A bangare guda, Manchester United ta ci tarar Lukaku saboda kin halartar atisaye tare da sauran ‘yan wasan kungiyar, inda a maimakon haka ya je ya yi atisaye tare da tsohuwar kungiyarsa ta Anderlecht a tsawon kwanaki biyu da suka shude.