Jaridar wasanni ta ‘Sport’ da ke Spain, ta rawaito cewar, sakamakon kaguwar da kungiyar ta PSG tayi kan saida Neymar, ta baiwa Manchester United damar daukarsa a matsayin aro kan euro miliyan 20.
Matakin na PSG ya sake bayyana tsamin dangantakar da ke tsakaninta da Neymar, wadda sai a shekarar 2022, yarjejeniyar da suka kulla kan euro miliyan 222 za ta kare.
An dai shafe watanni ana ce-ce-kuce tsakanin Neymar da kungiyar tasa da kuma sauran masu bibiyar lamurann wasanni, kan bukatar da dan wasan ya gabatar na son komawa tsohuwar kungiyarsa Barcelona da ya raba gari da ita a 2017.
A baya bayan nan kuma an rawaito cewa Barcelonan ta soma shirin ganin maido da Neymar gareta ko da kuwa a matsayin aro, kafin tabbatuwarsake daukarsa.