Isa ga babban shafi
Wasanni

Maguire ya zama mai tsaron baya mafi tsada a duniya

Harry Maguire ya kafa tarihin zama dan wasa mai tsaron baya mafi tsada a duniya, bayan da Manchester United ta kulla yarjejeniya da shi kan fam miliyan 80, kwatankwacin dala miliyan 97, a nairar Najeriya kuma, biliyan 35, da miliyan 160 da kuma dubu 400 kenan.

Harry Maguire, dan wasa mai tsaron baya mafi tsada a duniya.
Harry Maguire, dan wasa mai tsaron baya mafi tsada a duniya. Reuters/Ed Sykes
Talla

Karkashin yarjejeniyar, tsohon mai tsaron bayan na kungiyar Leicester City zai shafe shekaru 6 yana takawa United leda, tare da zabin kara wa’adin zuwa shekaru 7.

Sauyin shekar da Maguire mai shekaru 26 yayi, ya sanya shi zarta tsadar mai tsaron baya Virgil Van Djik da Liverpool ta sayo daga Southampton kan fam miliyan 75 a watan Janairu na shekarar 2018.

To a halin yanzu dai sauran ‘yan wasan masu tsaron baya da suka fi takwarorinsu tsada a duniya baya ga harry Maguire da Virgil Van Djik, sun hada da Lucas Hernandez da ya koma Bayern Munich daga Atletico Madrid kan fam miliyan 68 a Yulin da ya gabata, da kuma Matthijs De Ligt da ya koma Juventus daga Ajax kan fam miliyan 67 da rabi shi a watan Yulin.

Mai tsaron baya na biyar mafi tsada shi ne Aymeric Laporte da ya koma Manchester City daga Athletic Bilbao kan fam miliyan 57 a watan Janairu na 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.