Isa ga babban shafi
Wasanni

Kocin Juventus na zuke taba sigari sama da dubu 21 a shekara 1

Sabon kocin Juventus Maurizo Sarri ya sha alwashin daina busa taba sigari, halayyar da ta zame masa jiki a baya.

Tsohon kocin kungiyar Napoli, mai horas da Juventus a yanzu, Maurizio Sarri.
Tsohon kocin kungiyar Napoli, mai horas da Juventus a yanzu, Maurizio Sarri. AFP
Talla

Yayin wata ganawa da manema labarai, Sarri yace a kowace rana yana zuge karan sigari 60.

Idan aka fadada lissafin yawan sigarin da kocin mai shekaru 60 ke zukewa, a mako daya Maurizio Sarri na shan kara 420, a wata daya kuma yana gamawa da kara dubu 1 da 825.

A shekara guda kuma kocin na Juventus yana zuke karan taba sigari dubu 21,900.

Abin da yafi daukar hankali dangane da halayyar mai horaswar kan yawaita shan tabar, shi ne yadda kididdiga ta nuna cewa a shekara daya yana kashe fam dubu 17,000 kan sayenta, kwatankwacin naira miliyan 7 da dubu 661 da dari 595 da kwabo 80.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.