Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya kauce wa tuhuma kan fyade a Amurka

Dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ba zai fuskanci tuhuma ba kan zargin da ake yi masa na yi wa wata mace fyade shekaru 10 da suka gabata a Las Vegas na Amurka, bayan masu shigar da kara na gwamnati sun ce, babu isassun shaidun da za su basu damar ci gaba da tuhumar sa.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Kathryn Mayorga, tsohuwar taurauruwar kuma malamar makaranta ta ce, gwarzon dan wasan ya yi mata fyade a shekarar 2009 a wani Otel da ke Lasa Vegas, inda bayan shekara guda da aukuwar lamarin, dan wasan ya cimma yarjejeniyar biyan ta kudin toshiyar baki domin hana ta fallasa lamarin.

Sai dai dan wasan wanda ya taka leda a Real Madrid da Manchester United, ya musanta zargin yi mata fyade ,yana mai cewa, da amincewarta ya tara da ita.

Mujallar Der Spiegel ta Jamus wadda ta fara fallasa labarin fyaden ga duniya, ta ce, Ronaldo ya yi tayin bai wa Mayorga Dala dubu 375 don yin shiru da bakinta.

Sai dai lauyan Mayorga ya ce, tsohuwar tauraruwar ta samu kwarin guiwar fallasa labarin ne sakamakon gangamin #MeToo wanda ya bai wa mata kwarin guiwar bayyana irin cin zarafin da suka fuskanta daga maza a rayuwarsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.