Isa ga babban shafi
Wasanni

Ighalo ya yi gaggawar rataye takalmansa- Babangida

Tsohon fitaccen dan wasan Super Eagles, Tijjani Babangida ya bayyana cewa, Odion Ighalo ya yi gaggawar rataye takalmansa a matakin wasan kasa da kasa.

Odion Ighalo na Najeriya
Odion Ighalo na Najeriya Ben STANSALL / AFP
Talla

Ighalo da ya lashe kyautar takalmin zinari a Gasar Cin Kofin Kasashen Afrika da aka gudanar a Masar, ya sanar da ritayarsa daga buga wa Najeriya kwallon kafa.

Sai dai Tijjani Babangida ya bayyana cewa, yana da shakku game da sahihancin labarin ritayar Ighalo, amma muddin labarin ya zama gaskiya, to lallai ya kamata a dakatar da shi daga ritayarsa domin kuwa a halin yanzu babu wanda zai iya maye gurbinsa a tawagar Super Eagles.

Babangida ya bayyana Ighalo a matsayin kwararren dan wasan gaba da tauraronsa ke haskawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.