Isa ga babban shafi
Wasanni

Gareth Bale na gab da raba gari da Real Madrid

Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa, Gareth Bale na gab da raba gari da kungiyar.

Gareth Bale na Madrid
Gareth Bale na Madrid REUTERS/Javier Barbancho
Talla

Dan wasan mai shekaru 30 bai buga wasan da Madrid ta sha kashi ba a hannun Bayern Munich da ci 3-1 a wasan share fagen shiga sabuwar kaka a Amurka.

Bayan wannan fafatawar ce, Zidane ya bayyana cewa, suna fatan Bale zai bar kungiyar nan ba da jimawa ba, matakin da ya ce, shi ya fi dacewa ga kowa, kuma a halin yanzu suna kan aikin cefanar da shi ga wata kungiya.

Bayanai na cewa, kungiyar kwallon kafa ta Beijing Guoan da ke buga gasar Super League ta China, ita ce ke muradin sayen Gareth Bale daga Madrid, inda ta shirya biyan sa albashin da ya fi na kowanne dan wasa tsoka a tarihin kwallon kafar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.