Isa ga babban shafi

Senegal da Algeria sun shirya don karawa a wasan karshe na AFCON

Tsaffin abokanai 2 Djamel Belmadi na Aljeriya da Aliou Cisse na Senegal za su jagoranci kasashensu zuwa wasan karshe na lashe kofin Afrika da ke gudana can a kasar Masar, gasar da a wannan karon ta zo abubuwan mamaki.

Kofin gasar AFCON
Kofin gasar AFCON SuperSport
Talla

Belmadi da Cisse dukkanninsu wadanda suka taka leda a bangaren kasashensu kafin barinsu tamaula a shekarar 2002 na daga cikin ‘yan wasan da suka kara da juna yayin makamanciyar gasar a shekarar 1990, shekarar da Aljeriyan ta dage kofin bayan lallasa Najeriya a wasan karshe.

A bangaren guda wasan na yau, zai hada gwaraza biyu daga kungiyoyi masu doka gasar Firimiya 2 da ke dabi da juna, wato Sadio Mane na Liverpool da Riyad Maharez na Manchester City.

Cikin haduwa 22 da kasashen biyu suka yi a Tarihi, Algeria ce ta yi nasara kan Senegal, har sau 13 inda ko a wasan rukuni ma Algerian ta zura kwallo guda a ragar Senegal ranar 27 ga watan Yuni, kwatankwacin wanda ta yi mata a shekarar 1990.

A bangare guda Senegal ba ta taba yin nasara a kan Algeria a gasar cin kofin Afrika ba, cikin wasanni 8 da suka buga tare a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.