Isa ga babban shafi
Wasanni

Damben Boksin: Mayweather ba zai sake dambacewa da Pacquiao ba

Wani na kusa da shahararren dan wasan damban boxing din nan Floyd Mayweather, mai suna Leonard Ellerby ya tabbatar da cewa dan damben boksin din ba zai maimaita dambe da Manny Pacquiao ba.

Floyd Mayweather bayan wata nasarar da ya samu kan  Conor McGregor, a shekarar 2017.
Floyd Mayweather bayan wata nasarar da ya samu kan Conor McGregor, a shekarar 2017. GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP
Talla

Wani na kusa da shahararren dan wasan damban boxing din nan Floyd Mayweather, mai suna Leonard Ellerby ya tabbatar da cewa dan damben boksin din ba zai maimaita dambe da Manny Pacquiao ba.

Ellerby, wanda shi ke tafiyar da harkokin Mayweather ya shaida wa wata kafar yada labaran damben boksin cewa ko da za a ninka kudin da ya samu a wancan damben na farko da ya yi da Pacquaio ne ba zai kwadaitu ba.

An yi amannan cewa Mayweather ya samu akalla dala miliyan dari 3 a nasarar da ya samu kan Pacquiao, wanda damben da aka fi samun kudi kenan a tarihin damben boxing, inda mutum guda ya shake wadannan makudan kudi, kuma an samu kudin shiga da ya kai dala miliyan dari 6 a wannan damben.

A bangare daya kuwa, mai horar da Pacquiao Freddie Roach, a makon da ya gabata, ya ce yana daukin a ce gwanin damben, dan kasar Pillipines ya amince da sake wannan wasa, bayan dukan kawo wuka da ya sha a hannun Mayweather.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.