Isa ga babban shafi
Wasanni

Kotun Najeriya ta bayar da umarnin cafke jagororin NFF

Babbar kotun Najeriya ta bayar da umarnin cafke wasu daga cikin jiga-jigan Hukumar Kwallon Kafar Kasar bisa zargin su da ruf da ciki da Dala miliyan 8.4 da Hukumar FIFA ta bai wa Najeriya a matsayin ladar halartar gasar cin kofin duniya da aka gudanar a shekarar 2014 a Brazil.

Shugaban Hukumar NFF, Amaju Pinnick tare da shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban Hukumar NFF, Amaju Pinnick tare da shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Kotun ta bayar da sammacin kama mataimaka biyu na shugaban Hukumar ta NFF, Seyi Akinwumi da Shehu Dikko da Ahmed Yusuf da ke cikin kwamitin zartaswar hukumar, sai kuma Sakatare Janar na Hukumar wato, Mohammad Sanunsi.

Kotun na tuhumar wadannan mutane hudu tare da shugaban NFF, Amaju Pinnick da a yanzu haka ke halartar gasar cin kofin kasashen Afrika a kasar Masar.

Kodayake kotun ta dage zaman tuhumar jagororin na NFF a ranar Litinin bayan sun gaza bayyana a gaban kotun.

Kotun ta ayyana ranar 26 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a ci gaba da zaman sauraren shari’ar , yayinda ya zama dole su bayyana a gabanta a wannan karo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.