Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Mata zai ci gaba da zama a Man Utd har zuwa 2021

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta baiwa dan wasanta, Juan Mata sabon kwantiragin da zai rike shi a kungiyar har zuwa shekarar 2021.

Juan Mata yayin da ya ci kwallo a wasa tsakanin Man Utd da Norwich
Juan Mata yayin da ya ci kwallo a wasa tsakanin Man Utd da Norwich Reuters / John Sibley
Talla

Kafin yanzu, Mata mai shekaru 31 yana da damar tattaunawa da wasu kungiyoyi, duba da cewa kwantiraginsa na karewa a wannan watan Yunin da muke ciki, kuma basu kai ga matsaya ba a tattaunawarsu da United.

Sai dai bayan Ander Herrera da Antonio Valencia duk suka bar kungiyar a karshen wannan kaka ba tare da ta samu ko kwandala ba, United ta dage har sai da ta rike Mata.

A shekaru biyar da ya shafe yana murza wa kungiyar tamaula, Mata ya ci kwallaye 45 a wasanni 218 da ya buga mata, kana ya ci kofin Europa da FA da kuma League Cup.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.