Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

'Yan wasan Super Eagles 10 na jinya gab da fara gasar cin kofin Afrika

Akalla ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta super eagles 10 ne ynzu haka ke jinya gabanin fara gasar cin kofin Afrika a ranar juma’a 21 ga watan Yunin nan da muke ciki.

Mai horar da kungiyar Super Eagles Gernot Rohr tare da wasu 'yan wasansa
Mai horar da kungiyar Super Eagles Gernot Rohr tare da wasu 'yan wasansa Reuters
Talla

A ranar Asabar 22 ga wata ne Najeriyar za ta fara wasanta na farko inda za ta kara da Burundi, dai dai lokacin da ta ke fatan dage kofin a wannan karon bayan fashin shekaru 4 ba a ga kafarta a gasar ba.

Wasu rahotanni na nuni da cewa rashin lafiyar ‘yan wasan na da alaka da iskar da suka shaka ta naurar sanyaya dakin wani otel, kuma ‘yan wasan da yanzu haka ke kwance sun hada da Ahmed Musa da Shehu Abdullahi da Leon Balogun da Henry Onyekuru da kuma Chidozie Awaziem.

Za a iya cewa dai rashin lafiyar wadannan ‘yan wasa babban kalubale ne ga wasannin da ke gaban Najeriya a gasar bayan rashin nasarar su hannun Senegal da kwallo daya da nema ranar Lahadi a wasan sada zumunta.

Bayan wasansu na ranar Asabar da Burundi a ranar 26 ne Super Eagles za ta kara da Guinea kafin daga bisani ta karkare wasanta na rukuni da Madagascar ranar 30 ga watan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.