Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

PSG ta nuna bukatar rabuwa da Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta ce ta fara duba yiwuwar sayar da dan wasanta mafi tsada a duniya wato Neymar Junior inda shugaban Club din Nasser Al-Khelaifi ke cewa munanan dabi’u da rashin da’ar dan wasan baa bin jura ba ne.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar Junior
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar Junior REUTERS/Ricardo Moraes
Talla

Neymar dan Brazil mai shekaru 27 wanda ya koma PSG daga Barcelona cikin watan Agustan shekarar 2017 kan kudi yuro miliyan 222, cikin kakar wasan da ta gabata kwallaye 15 kadai ya iya nasarar zurawa cikin wasanni 17 da ya doka, sakamakon yadda ya rika fuskantar dakatarwa baya ga jinyar watanni da ya shafe ya na yi.

Wasu jaridun Faransa sun ruwaito shugaban Club din na PSG na cewa, a shirye su ke su sayar da Neymar cikin wannan kakar musayar ‘yan wasan mayukar suka samu tayi mai kyau daga wata kungiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.