Isa ga babban shafi
Wasanni

Pillars za ta biya tarar naira miliyan 8 saboda tayarda hatsaniya

Hukumar LMC da ke shirya gasar Premier ta Najeriya, ta ci tarar Kano Pillars naira miliyan 8, tare da haramtawa kaftin din kungiyar Rabi’u Ali buga wasani 12.

Kaftin din kungiyar Kano Pillars Rabi’u Ali da hukumar LMC ta haramtawa buga wasanni 12.
Kaftin din kungiyar Kano Pillars Rabi’u Ali da hukumar LMC ta haramtawa buga wasanni 12. Vanguard News
Talla

Matakin ya biyo bayan samun kaftin din na Kano Pillars da laifin tunzura magoya bayansu da suka tayarda da hatsaniya, tare da cin zarafin alkalin wasa Adebimpe Guadri a ranar litinin da ta gabata, yayin wasan Super Six da Pillars din suka tashi 1-1 da Enugu Rangers.

Yayin wasan dai Rabi’u Ali ya tunkari alkalin wasa ne da zummar nuna bacin rai kan rashin adalcin da yake ganin yana yiwa kungiyar tasa lamarin da ya kai ga jefa musu kwallo a raga, hakan ya baiwa wasu magoya damar afkawa cikin fili, tare da soma jifa.

Baya ga biyan tarar ta naira miliyan 8 da kuma haramtawa kaftin dinta buga wasanni 12, Kano Pillars za ta buga wasanninta na gaba a gida ba tare da yan kallo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.