Isa ga babban shafi
Wasanni

Hatsaniya ta kaure a wasan Kano Pillars a Lagos

An samu hatsaniya a wasan da aka kece raini tsakanin Kano Pillars da Rangers a gasar zaratan kungiyoyi shida da ke taka leda a firimiyar Najeriya da ake gudanarwa a birnin Lagos.

Wasu daga cikin 'yan wasan Kano Pillars a filin wasa na garin Agege da ke jihar Lagos a Najeriya
Wasu daga cikin 'yan wasan Kano Pillars a filin wasa na garin Agege da ke jihar Lagos a Najeriya Naija news
Talla

Rahotanni sun ce, magoya bayan Kano Pillars sun kai hari kan hukumomin da ke kula da gasar bayan kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki 1-1 a ranar Litinin.

Pillars ce ta fara jefa kwallon farko a minti na 59 ta hannun kaften dinta Rabiu Ali, sai dai a daidai lokacin da ake gab da tashi wasan, Rangers ta farke ta hanyar bugun fanaritin da ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya.

Bayan tashi wasan ne, Rabiu Ali ya tunkari alkalin wasan cikin fushi domin nuna rashin jin dadinsa da tsawaita lokaci a zagaye na biyu na wasan da aka yi a garin Agege.

Hakan ne yasa magoya bayan Pillars su ma suka fantsama cikin filin wasan tare da jefe-jefen duwatsu da wasu karikitai. Sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar kwashe hukumomin da ke kula da wannan gasa ba tare da yi musu lahani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.