Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya lashe kyautar takalmin zinaren gasar zakarun Turai

Kaftin din Barcelona Lionel Messi, ya lashe kyautar takalmin zinare na gasar zakarun Turai ta bana, bayan nasarar zama dan wasan da ke gaba wajen yawan kwallaye a gasar.

Kaftin din Barcelona Lionel Messi.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi. REUTERS/Albert Gea
Talla

Messi dai na da jimillar kwallaye 12 a gasar ta bana, yayinda dan wasan gaba na Bayern Munich Robert Lewandowski ke biye masa a matsayi na 2 da kwallaye 8.

Sergio Aguero na Manchester City, Moussa Marega na FC Porto, Dusan Tadic na Ajax da kuma Crsitiano Ronaldo na Juventus, dukkanin na da kwallaye 6, a matsayi na uku.

Sauran 'yan wasan da ke biye wajen yawan kwallayen da suka ci wa kungiyoyinsu, sun hada da Lucas na Tottenham, Neymar na PSG, Sterling na Manchester City, da Muhammad Salah na Liverpool, saikuma Dybala da Harry Kane na kungiyar Tottenham, wadanda kuma dukkaninsu ke da kwallaye 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.