Isa ga babban shafi
Wasanni

Senegal da Italiya sun yiwa takwarorinsu zarra a Poland

Senegal da Italiya sun zama kasashe na farko da suka samu nasarar kaiwa zagaye na 2, na gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 da kasar Poland ke karbar bakunci.

Yan wasan kasar Senegal yayin murnar samun nasara a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20.
Yan wasan kasar Senegal yayin murnar samun nasara a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20. Getty Images
Talla

Kasashen biyu sun samu nasarar ce, bayan buga wasanni 2 daga cikin uku da kowannensu yayi a rukunin da yake ciki.

A wasanta na farko a rukunin A, Senegal ta lallasa Tahiti da 3-0, yayinda kuma a wasa na 2, ta lallasa Colombia da 2-0.

A halin yanzu kuma Senegal din ce ke jagorantar rukunin na A da maki 6, Poland mai masaukin baki na biye mata da maki 3, Colombia maki 3, sai kuma Tahiti ta karshe ba ta maki.

A rukunin B kuwa a wasanta na farko Italiya ta samu nasara kan Mexico da 2-1, sai kuma wasa na biyu da samu nasara kan Ecuador da 1-0.

Italiyar ce ke jagorantar rukunin na B da maki 6,Japan ke biye da ita da maki 4, Ecuador da maki 1, sai kuma Mexico ta karshe ba ta da maki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.