Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Roberto Firmino na Liverpool ya murmure daga jinyar rauni

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta ce dan wasanta na gaba Roberto Firmino ya murmure daga raunin da ya samu, inda ya dawo filin atisaye yau Talata a Marbella.

Dan wasan gaba na Liverpool Roberto Firmino
Dan wasan gaba na Liverpool Roberto Firmino REUTERS/Andrew Yates
Talla

Firmino dan Brazil mai shekaru 27 wanda ya rasa wasannin Club din har 3 karkashin gasar Firimiya sanadiyyar raunin, yanzu haka Club din ya bayyana cewa ya na da cikakkiyar lafiyar taka leda a wasan karshe da Liverpool za ta kara da Tottenham.

Bayan rashin nasarar dage kofin Firimiya da tazarar maki tsakaninta da Manchester City, tawagar ‘yan wasan Jurgen Klopp 26 sun fara atisayensu na hutun karshen kaka a Marbella yau Talata kafin dawowa Ingila a nan da kwanaki 6 don fara shirin tunkarar wasan karshe na cin kofin zakarun Turai da zai gudana a birnin Madrid na Spain ranar 1 ga watan Yuni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.