Isa ga babban shafi
Wasanni

Bana fargabar rabuwa da kwararrun 'yan wasa - Erik ten Hag

Mai horas da kungiyar Ajax, Erik ten Hag, ya ce ko kadan baya fargabar rabuwa da kwararrun ‘yan wasansa, biyo bayan sauyen shekar da wasunsu za su yi zuwa wasu manyan kungiyoyin nahiyar Turai.

Mai horas da kungiyar Ajax Erik ten Hag bayan fitar da Juventus daga gasar Zakarun Turai.
Mai horas da kungiyar Ajax Erik ten Hag bayan fitar da Juventus daga gasar Zakarun Turai. REUTERS/Alberto Lingria
Talla

Erik ten Hag ya bayyana haka ne, bayan bikin mikawa kungiyar ta Ajax kofin gasar kwallon kafa ta kasar Holland da ta lashe a bana, inda magoya bayansu akalla dubu 60 suka halarci babban filin wasa da ke birnin Amsterdam.

Kocin na Ajax ya bayyana cewa bajintar da suka nuna a gasar Zakarun Turai ta bana, da suka kai zagayen kusa da na karshe ne ya sanya manyan kungiyoyi neman saye ‘yan wasansa, ammaduk da haka ya sha alwashin maimaita irin kwazon da suka nuna a gasar da ke tafe.

Tuni dai Barcelona ta saye Frenkie de Jong mai shekaru 22, da ke bugawa kungiyar ta Ajax bangaren tsakiya akan euro miliyan 86.

Karin kwararrun yan wasan kungiyar ta Ajax da ke shirin ficewa zuwa wasu manyan kungiyoyin sun hada da Mattijs de Ligt mai shekaru 19, Hakim Ziyech, David Neres, Donny van de Beek da kuma mai tsaron ragarsu Andre Onana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.