Chelsea ta dare matsayi na 3 a gasar Premier
Chelsea ta lallasa Watford da kwallaye 3-0, abinda ya bata damar komawa matsayi na 3 a gasar Premier.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Da fari yan wasan Chelsea da ke fafata wasan na ranar Lahadi a filin wasansu na Stamford Bridge sun fuskanci ihun kushewa daga magoya baya a zagayen farko, saboda gazawa wajen jefa kwallo a ragar abokiyar hamayyar ta su Watford.
Sai dai a zagaye na biyu labari ya sauya, inda cikin mintuna uku ‘yan wasan Chelsea Loftus-Cheek da Luiz suka jefa kwallaye 2; daga bisani kuma Gonzalo Higuain ya jefa kwallo ta uku.
Idan har Chelsea ta samu nasarar lashe wasan karshe na gasar Premier ta bana da za ta fafata da Leicester City a ranar Lahadi mai zuwa, hakan zai tabbatar mata da tikitin halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta badi.
To amma kafin yin tattaki zuwa Liecester City, Chelsea za ta karbi bakuncin Frankfurt domin fafata zagaye na biyu, na wasan kusa da na karshe a gasar Europa.
A wasan farko an tashi kunnen doki 1-1, tsakanin kungiyoyin a Jamus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu