Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Barcelona ta fitar da Manchester United daga gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi waje da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United daga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai zagayen wasan gab da na kusa da na karshe.

Lionel Messi na Barcelona bayan nasarar zura kwallo a ragar Manchester United
Lionel Messi na Barcelona bayan nasarar zura kwallo a ragar Manchester United Reuters/John Sibley Livepic
Talla

An dai kammala wasa Barca na da jumullar kwallaye 5 da banza kan Man U, bayan zura mata kwallaye har 3 a jiya ka na kuma ga guda na makon jiya da ta zura mata har gida wanda ke matsayin biyu.

Yayin wasan na jiya Lionel Messi ne ya zura kwallaye har 2 cikin minti na 20 da fara wasa kafin daga bisani Cautinho ya kara ta 3 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, ba kuma tare da United ta iya ramawa ba.

Yanzu haka dai Barca na dakon wadda za ta yi nasara tsakanin Liverpool da FC Porto don karawa a wasan gab da na karshe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.