Isa ga babban shafi
wasanni

Arsenal da Liverpool sun koka kan cin zarafin 'yan wasa

Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal ta fara gudanar da bincike bayan wani hoton bidiyo ya nuna daya daga cikin magoya bayanta na cin zarafin dan wasan baya na Napoli, wato Kalidou Koulibaly a yayin fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a gasar Europa Lig.

Kalidou Koulibaly na Napoli da magoya bayan Arsenal suka ci zarafinsa
Kalidou Koulibaly na Napoli da magoya bayan Arsenal suka ci zarafinsa REUTERS/Ciro De Luca
Talla

Arsenal wadda ta samu nasara da ci 2-0 a karawar, ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, ta yi tir da irin wannan cin zarafin na nuna wariyar launin fata, kuma za ta binciko wanda ya aikata haka.

A bangare guda, shi ma kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya yi tir da zagin wariyar jinsi da aka yi wa Mohammed Salah na Masar, kuma ya bukaci haramcin har abada kan magoya bayan Chelsea da suka ci mutuncin Salah.

Wani hoton bidiyo ya nuna mutane shida magoya bayan Chelsea na kiran Salah da mai "kaddamar da hare-haren bama-bamai"

Wannan matalar ta nuna wariyar launin fata na ci gaba da karuwa, domin ko a ‘yan kwanakin nan, sai da aka yi wa ‘yan wasan Ingila a Gasar Neman Tikitin Shiga Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta 2020, in da aka yi ta alakanta su da birai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.