Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Inter Milan na shirin daukar Antonio Conte a matsayin Manaja

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan mai doka gasar Seria A ta Italiya na shirin kulla kwantiragi da tsohon Manajan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Antonio Conte.

Antonio Conte
Antonio Conte Reuters/Alessandro Garofalo
Talla

Rahotanni sun ce Steven Zhang shugaban Inter Milan da kansa ya ce a shirye ya ke ya biyan kowanne irin kudi don daukar Conte mai shekaru 49.

Conte, wanda ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Juventus tsawon shekaru 2 kafin karbar ragamar horar da kungiyar kwallon kafar kasar Italiya, kawo yanzu ya horar da kungiyoyin kwallon kafa har 8 amma daya ce cal a wajen Italiya wato Chelsea.

Sai dai da alama Conte bashi da bukatar komawa Italiyan, dalili kenan da ake ganin ya sanya shi gindaya sharadin biyansa yuro miliyan 9 a matsayin albashinsa kowacce shekara baya ga biya masa haraji, wanda kuma idan har Intermilan ta amince zai dara takwaransa na Juventus Massimiliano Allegri wanda ke matsayin Koci mafi daukar albashi a Italiyan.

Ka zalika matukar Inter Milan ta amince da daukar Conte, hakan na nuna cewa za ta iya yin asarar yuro miliyan 21 wajen sallamar Spalletti wanda sai a shekarar 2021 ne kwantiraginsa zai kare.

Yanzu haka dai Spalleti ya kai Inter Milan matsayin ta 3 a taburin gasar Serie A ko da dai akwai tazarar maki 27 tsakaninta da Jagora Juventus, yayinda su ke da sauran wasanni 7 kafin karkare gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.