Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo zai yi jinyar sama da makwanni 6

Rahotanni daga kasar Italiya sun tabbatar cewa tauraron dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo, zai jinyar makwanni takwas, kafin dawowa wasa.

Cristiano Ronaldo bayan samun rauni, a wasan da kasarsa ta Portugal ta fafata da Serbia.
Cristiano Ronaldo bayan samun rauni, a wasan da kasarsa ta Portugal ta fafata da Serbia. REUTERS/Rafael Marchante
Talla

A karshen watan Maris da ya gabata, Ronaldo yasamu rauni a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Turai, da kasarsa Portugal ta buga da Serbia, wanda suka tashi 1-1.

Hakan na nufin Ronaldo ba zai damar buga wasanni biyu da Juventus za ta fafata da Ajax ba a zagayen kwata final na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Zalika Ronaldo ba zai buga wasanin gasar Seria A da Juventus za ta fafata da kungiyoyin Cagliari, AC Milan, SPAL, Forentina, Inter Milan, Torino, AS Roma, Atalanta da kuma Sampdoria ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.