Isa ga babban shafi
Wasanni

UEFA za ta ci tarar Ronaldo kan salonsa na murnar cin kwallo

Hukumar kula da kwalon kafa ta nahiyar Turai UEFA ta tsaida 21 ga watan Maris da muke, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan laifin da ta ce dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya aikata.

Cristiano Ronaldo yayin murnar lallasa Atletico Madrid a gasar Zakarun Nahiyar Turai ta 2019.
Cristiano Ronaldo yayin murnar lallasa Atletico Madrid a gasar Zakarun Nahiyar Turai ta 2019. REUTERS/Alberto Lingria
Talla

Kwamitin ladabtarwa na hukumar ta UEFA ya samu Ronaldo ne da laifin nuna salon murna na tsokana ta hanyar kama gabansa, bayan zura kwallaye uku ragar Atletico Madrid yayin fafata wasan gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wanda ya yi sanadin fitar da su daga gasar.

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya soma nuna murnar lallasa Juventus da irin wannan salo, bayan samun nasara kansu da kwallaye 2-0 a zagayen farko na matakin kungiyoyi 16 a gasar ta zakarun Turai.

Bayan fafatawar kungiyoyin a zagayen farko dai, UEFA ta ci tarar kocin na Atletico Madrid tarar euro dubu 20, inda yayi sa’ar tsallake hukuncin dakatar da shi da aka yi zaton za ta dauka da fari.

Duk da waccan mataki da UEFA ta dauka kan Simeone, sai gashi, Cristiano Ronaldo ya nuna salon murnar na tsokana a matsayin ramuwa, bayan zura kwallaye uku a ragar Atletico, abinda yayi sanadin fitar da su baki daya daga gasar zakarun Turan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.