Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 21/05 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 21/05 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 21/05 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 21/05 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/05 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/05 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/05 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/05 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/05 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/05 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/05 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Wasanni

Zidane ya sake karbar jagorancin horar da Real Madrid

media Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane. Reuters/Albert Gea

Zinaden Zidane ya sake karbar ragamar horar da Real Madrid a ranar Litinin watanni 9 bayan ajiye aikin horar da kungiyar bisa radin kansa, lokacin da ya jagoranceta lashe kofin gasar zakarun Turai sau 3 a jere.

Komen na Zidane ya biyo bayan sallamar kocinta Santiago Solari da Madrid din ta yi, inda ta sake kulla yarjejeniyar shekaru uku da Zidane, da za ta kare a ranar 30 ga watan Yuni, na shekarar 2022.

Zidane ya komawa Real Madrid a daidai lokacin da ya rage wasanni 11 kawai a kammala gasar La Liga ta bana, wadda kungiyar ke matakin ta uku da maki 51, tazarar maki 12 tsakaninta da babbar abokiyar hamayya Barcelona da ke jagorantar La Ligar da maki 63.

Matakin na Zidane dai ya zowa da dama a ba zata, la’akari da cewa a waccan lokacin da ya ajiye aikinsa, ya bar kungiyar ne a matsayi mai kyau, cike da samun nasarori, amma a yanzu ya karbe ta tana cikin halin kaka nika yi.

Sai dai yayin zantawa da manema labarai, Zidane ya ce ya yanke shawarar dawowa Madrid saboda kaunar kungiyar da yake da kishinta, dan haka a lokacin da shugabanta Florentino Perez ya tuntube shi, sai ya kasa kin amsa bukatar.

Tun a lokacin da Barcelona ta lallasa Real Madrid a jere a gasar la Liga da ta Copa del Rey aka sa ran za a kori kocin Madrid a wannan lokaci wato Santiago Solari, amma sai aka jinkirta, daga bisani kuma Ajax ta fitar da ita daga gasar zakarun Turai, lamarin ya sa ta tabbata Real Madrid ta yi barin Kofuna uku cikin mako 1.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure