Isa ga babban shafi
Wasanni

Wankin hula na neman kai Arsenal dare

Arsenal na fuskantar kalubale dangane da burin kaiwa zagayen kwata final a gasar Europa, bayan kayen da kungiyar ta sha a hannun Rennes da kwallaye 3-1 a Faransa.

Alkalin wasa Ivan Kruzliak yayin nunawa dan wasan Arsenal jan kati yayin fafatwarsu da kungiyar Rennes a gasar Europa.
Alkalin wasa Ivan Kruzliak yayin nunawa dan wasan Arsenal jan kati yayin fafatwarsu da kungiyar Rennes a gasar Europa. AFP
Talla

Da fari dai Arsenal ce ta soma jefa kwallo a ragar Rennes ta hannun dan wasan Alex Iwobi, amma daga bisani lissafi ya sauya, bayan da alkalin wasa ya baiwa mai tsaron baya na Arsenal Sokratis jan kati.

‘Yan wasan Rennes Benjamin Bourigeaud da Isma’ila Sarr suka ci wa kungiyar ta su kwallaye biyu, yayinda Nacho Monreal na Arsenal ya jefa kwallo a ragarsu bisa kuskure, abinda ya baiwa Rennes nasara kansu da kwallayen 3-1.

Muddin Arsenal na son kaiwa matakin gaba, tilas ta samu nasara kan Rennes da kwallaye 2-0 ko sama da haka, a fafatawar da za su yi zagaye na biyu a birnin London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.