Isa ga babban shafi
Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Juventus na fuskantar kalubale a gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus na fuskantar gagarumin kalubale duk da kasancewarta jagora a gida, kuma wadda ke kokarin lashe kofin Serie A karo na 8 a jere, amma akwai matsalar ko dai ta yi nasara kan Atletico Madrid ko kuma kai tsaye ta fice daga gasar zakarun Turai da Club din ke fatan lashewa tsawon shekaru.

Juventus dai na da zabin ko dai ta yi kokarin yin nasara kan Atletico a zagaye na 2 na wasannin zagayen kungiyoyin 16 ko kuma kai tsaye Atletico ta cire a matakin wanda ke matsayin kasa da matakin da ta kai a bara
Juventus dai na da zabin ko dai ta yi kokarin yin nasara kan Atletico a zagaye na 2 na wasannin zagayen kungiyoyin 16 ko kuma kai tsaye Atletico ta cire a matakin wanda ke matsayin kasa da matakin da ta kai a bara Stefani Rellandini/Reuters
Talla

Yayin zagayen farko na wasan kungiyoyi 16 dai Atletico ce ta yi nasara kan Juventus da kwallaye 2 da banza, inda a yanzu kuma Juventus ke bukatar gagarumar nasara matukar ta na fatan tsallakewa zuwa wasan gab da na kusa da na karshe na cin kofin.

Manajan Club din Massimiliano Allegri wanda ta kai shi ga samun matsala da shugaban Juventus bayan nasarar Atletico kan Club din da kwallo 2 da banza, ya ce a wasan wanda ke tunkaro su nan a ranar 12 ga watan nan, dole ne su yi nasara don ka iwa ga mataki na gaba.

A cewar Manajan sun koyi babban darasi daga wasan Madrid da Ajax matakin da ya kara musu kwarin gwiwar shiryawa tunkarar wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.