Isa ga babban shafi
Wasanni

Wakilin Bale ya zargi magoya bayan Real Madrid da nuna butulci

Wakilin dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale, yayi amfani da kakkausan harshe wajen sukar magoya bayan kungiyar, kan yadda suka rika yiwa Bale din ihu, yayin wasan El Clasico da Barcelona ta samu nasara kan Real Madrid a gidanta da 1-0.

Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale.
Dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale. REUTERS/Javier Barbancho
Talla

Duk da cewa yayin wasan na El Clasico da ya gudana a ranar Asabar Bale ya gaza nuna bajinta, wakilinsa Jonathan Barnett, ya zargi magoya bayan Madrid da butulci, la’akari da gagarumar gudunmawar da Bale ya baiwa kungiyar na ci mata kwallaye a wasannin karshe na gasar zakarun turai a shekarun 2014 da 2018.

Ihun da magoya bayan Real Madrid suka yiwa Bale yayin fafatwarsu da Barcelona ya zo ne mako daya, bayan da ya fuskanci suka kan yadda yaki nuna murna kan kwallon da ya jefa a ragar kungiyar Levante.

A kakar wasa ta bana dai Gareth Bale ya ci wa Real Madrid kwallaye 13 cikin wasanni 33 da ya buga, amma kocin kungiyar Santiago Solari, ya fi son fara wasa da Vinicious Junior da kuma Lucas Vazquez kafin baiwa Bale dama.

Wata majiya daga Real Madrid ta ce shugaban kungiyar Florentino Perez, yana shirin kakkabe ‘yan wasan kungiyar da dama da suka gaji, cikinsu kuma har da Gareth Bale, duk da cewa yarjejeniyarsa da kungiyar za ta kare ne a shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.