Isa ga babban shafi
Wasanni

Halartar bukukuwa ba zai shafi kwazona ba - Neymar

Dan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar, ya musanta cewa a yanzu yafi maida hankalinsa wajen shirya bukukuwan casu fiye da cimma burinsa na zama gagara-badau a duniyar kwallon kafa.

Dan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar, yayin bikin munar cikarsa shekaru 27.
Dan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar, yayin bikin munar cikarsa shekaru 27. THOMAS SAMSON/AFP/Getty Images
Talla

Neymar da ke kan jinyar makwanni 10 saboda raunin da ya samu a kafarsa cikin watan Janairu da ya gabata, ya shirya gagarumin bikin casu ne, na murnar cikarsa shekaru 27, wanda aka yi a birnin Paris.

Hakan yasa wasu da ke sukarsa bayyana shakku kan ko dan wasan zai iya jagorantar PSG zuwa matakin nasarar da take son kaiwa na lashe gasar Zakarun Turai, la’akari da cewa yawan bukukuwa da shaye-shaye kan shafi kwazon dan wasa, kamar yadda aka rawaito cewa, hakan na daga cikin dalilan da suka dusashe tauraron tsohon gwarzon dan kwallon kafa na duniya Ronaldinho.

Sai dai a martaninsa, Neymar ya ce rayuwarsa ta yau da kullum ta sha babban da rayuwarsa a fagen kwallon kafa, dan haka babu bangaren da zai shafi wani.

A cewar Neymar idan yana kan fili, kowa na da damar yi masa tambaya kan kwazonsa, amma fa idan ya fita gari, to ya kamata a shafa masa lafiya, a kuma kaucewa yi masa katsalandan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.