Isa ga babban shafi
Wasanni

Leicester City ta kori kocinta

Kungiyar Leicester City ta kori kocinta Claude Puel, kwana guda bayan kayen da ta sha a fafatawar ta da Crystal Palace a gasar Premier.

Claude Puel, kocin da Leicester City ta kora.
Claude Puel, kocin da Leicester City ta kora. Reuters/Andrew Couldridge
Talla

Yayin wasan da ya gudana a ranar Asabar, Crystal Palaca ta yi tattaki ne har filin wasan na Leicester King Power, ta kuma lallasa ta da kwallaye 4-1.

Kayen da Leicester ta sha a karshen makon ya sa a jimlace ta yi rashin nasara a sau biyar kenan daga cikin wasanni shidda da ta buga a baya bayan nan, sai kuma fitar da kungiyar ta Leicester daga gasar cin kofin FA a ranar 6 ga watan Janairu, a karkashin kocin na ta da ta kora Claude Puel, tare da mataimakinsa Jacky Bonnevay.

A halin yanzu mataimakan Puel a baya, da suka hada da Mike Stowell da Adam Sadler ne za su ci gaba da aikin horar da ‘yan wasan kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.