FIFA ta kakabawa Chelsea takunkumin sayen 'yan wasa
Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta haramtawa kungiyar Chelsea sayen ‘yan wasa, har sai an kammala cin kasuwar hada-hadar cinikin ‘yan wasan guda biyu nan gaba.
Wallafawa ranar:
Hukuncin na nufin Chelsea ba za ta sake sayen ‘yan wasa ba, har sai an shiga shekarar 2020, ko da yake kungiyar na da damar saida nasu ‘yan wasan.
FIFA ta kakabawa Chelsea takunkumin cinikin ‘yan wasan ne, bayan samunta da laifin saba ka’idar kulla yarjejeniya da wasu kananan ‘yan wasa da shekarunsu suka gaza kai ka’idar FIFA, da ta basu damar rattaba hannu kan yarjejeniya da wata kungiya.
Bayaga kakaba mata takunkumin cinikin ‘yan wasan, FIFA ta ci tarar Chelsea, dala dubu 600, sai dai kungiyar tana da damar daukaka kara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu