Isa ga babban shafi
Wasanni

Rashin Neymar zai shafi wasan PSG da United - Buffon

Mai tsaron ragar Paris Saint Germain Gianluigi Buffon ya bayyana fargaba kan yadda sakamakon wasan gasar zakarun Turai da za su fafata Yau Talata tsakaninsu da Manchester United.

Mai tsaron ragar PSG Gianluigi Buffon tare da dan wasan gaba na kungiyar Neymar.
Mai tsaron ragar PSG Gianluigi Buffon tare da dan wasan gaba na kungiyar Neymar. Regis Duvignau/Reuters
Talla

Buffon ya ce fargabar ta zama dole, ganin yadda kungiyar ta PSG za ta buga wasan ba tare da gwarzon dan wasanta ba wato Neymar.

Neymar ba zai samu bugawa PSG was aba har sai cikin watan Afrilu, saboda raunin da ya samu a kafafunsa, yayin wasansu da Starsbourg a cin kofin Faransa. Duk da cewa raunin bai kai ga yi masa tiyata ba, likitoci sun ce tilas ya yi jiyyar makwanni 10.

Buffon mai shekaru 41 ya dade yana fatan samun nasarar lashe kofin gasar zakarun Turai a kungiyoyin da ya bugawa, sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba, la’akari da cewa sau uku yana kaiwa wasan karshe, damarsa tana barewa.

To baya ga wasan PSG ta Manchester United, za a fafata tsakanin AS Roma da FC Porto a gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.