Isa ga babban shafi
wasanni

West Ham na bincike kan cin mutuncin Salah

Kungiyar Kwallon Kafa ta West Ham United na gudanar da bincike kan wani faifen bidiyo da ke nuna wani magoyin bayanta na muzanta dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah a yayin fafatawar da suka tashi kunnen doki 1-1 a ranar Litinin a gasar firimiyar Ingila.

Mohamed Salah na Liverpool
Mohamed Salah na Liverpool REUTERS/Darren Staples
Talla

An yi amfani da wayar hannu wajen daukar hoton Salah mai shekaru 26 a daidai lokacin da ke shirin buga kwallo daga gefen raga.

An yi wa hoton kwaskwarima dauke da wasu kalamai na muzantawa ga dan wasan da kuma addininsa na Islama.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, West Ham ta ce, ko kadan ba za ta amince da irin wannan dabi’ar ba ta cin mutuncin wani a filin wasanta ba.

Tuni aka sanar da jami’an ‘yan sanda game da wannan batu da masharhanta ke cewa, na haddasa fitina tsakanin al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.