Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Manchester City na gab da komawa Jagorar Firimiya -Guardiola

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce fargabarsa bayan rashin nasararsu a hannun Newcastle makon jiya ta kau bayan nasararsu kan Arsenal da kwallaye 3 da 1, matakin da ya ke cewa suna gab da dawowa matsayinsu na jagora a gasar.

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola REUTERS/Phil Noble
Talla

Bayan nasarar ta jiya da ta bai wa City maki 59 a wasa 25 da ta doka, ya nuna cewa yanzu tazarar maki 2 ne kacal tsakaninta da Liverpool jagora ko da dai ita Liverpool wasa 24 kadai ta doka.

Matukar dai Liverpool ta lallasa West Ham United za a iya cewa murnar Guardiola za ta koma ciki amma fa idan har West Ham ta lallasa Liverpool kai tsaye City ta koma matsayinta na Jagora.

West Ham din dai ita ke matsayin ta 12 a teburin na Firimiya da maki 31 bayan doka wasa 24, kuma ana ganin abu ne mai wuya ta iya yin nasara kan Liverpool a wasan na yau wanda ita ce za ta karbi bakonci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.