Tun a ranar 21 ga watan Janairun da ya gabata ne, jirgin ya yi batan-dabo bayan ya taso daga birnin Nantes na Faransa zuwa Cardiff na Ingila dauke da Sala da matukinsa, David Ibbotson.
Wani lokaci a yau ne ake sa ran masu bincike za su fadada bincikensu a magudanar ruwan da aka gano buraguzan jirgin a Ingila.
Kungiyar kwallon kafa ta Cardiff ta kulla kwantiragi da Sala akan farashin Pam miliyan 15, yayin da wannan ibtila’in ya rutsa da shi a daidai lokacin da yake kan hanyar zuwa kungiyar.